Yan takarar kansaloli sunyi zanga-zanga a jihar a garin Kaduna

Shugaban kungiyar yace abun da ya faru ranar zaben jagororin jam'iya na takarar kansaloli ba zabe bane, son sai aka yi

Yan takarar kansaloli na jam'iyar APC na Kaduna ta arewa sun nuna bacin ran su kan sakamakon fidda yan takarar jam'iya.

Kungiyar karkashin jagorancin shugabanta Aminu Adamu, sun gudanar da zanga-zangar lumana ranar Laraba don nuna fushin su da rashin amincewar su ga sakamakon zaben fidda da ‘yan takara na jam’iyyar da akayi makonni biyu da suka shude.

Yayin da ya gana da maneman labarai shugaban  ya bayyana  cewa abinda akayi ranar zaben gwanayen jam'iya ba zabe bane, kawai an zabi wadanda ake so.

"Alkawarin da gwamna El-Rufai yayi cewa gwamnati ko jami’an gwamnati ba za su sa ka baki ko hannu a zaben ba ne ya sa muka fito domin yin takarar kujerun kansila a gundumomin mu amma sai gashi wasu jami’an gwamnati sun zo sun dagula abin inda suka zabi nasu ba tare da an gudanar da zaben fidda dan takarar ba.

"Mun rubuta wa gwamnatin jihar domin ta dauki mataki kan haka amma shiru kake ji kamar an ci shirwa. Dalilin da ya sa ke nan muka fito wannan zanga-zanga da kuma bayyana wa gwamnati cewa akwai matsalar gaske idan fa jam’iyyar APC ta ce ta haka zata yi abubuwan ta"yace.

Sakataren jam’iyyar Yahaya Pate ya karyata wannan korafi, inda ya ce babu wani abu kamar haka da ya faru a kananan a zaben fidda dan takara na jam’iyyar.