Barayi sun kashe wani dan kasuwa dan kasar Syria, sun saci yaron sa

Masu garkuwan sun kai masa hari yayin da yake shirin kulle shagonsa a daren ranar talata

An wasu labarin wani dankasuwa dan kasar Syria  Ahmed Abu Areeda wanda masu garkuwa da mutane suka kashe a jihar Kano tare da sace yaron sa Muhammed Ahmed.

Kamar yadda wasu shaidar gani da ido suka sanar, yan fashin sun kashe shi ne yayin da yake kokarin daukar motar shi a dai dai ofishin sa dake titin Hospital road nan garin kano.

"Lamarin ya faru a daren ranar talata da misalin karfe 8 na dare bayan ya rufe shagon sa inda yan fashin suka shigo harabar inda yake cikin mota kirar Peuveot.

"Nan suka harbe shi har suka sace daya daga cikin yaran sa biyu dake tare dashi a lokacin. basu yi nasarar sacedayan yaron shi ba domin ya ruga ne yayin da suka shigo domin kiran makwabta." inji shaida.

Mai magana da yawun rundunara yan sanda ta jihar Kano Magaji Musa Majia ya tabbatar da faruwar hakan inda ya kara da cewa yan fashin sun kai masu hari ne domin sace yaran amma yayin yin haka suka kashe mahafinsu.

Yace har yanzu ana ba'a san inda aka tafi da yaron ba amma ana cigaba da bincike kan lamarin.