Eze-Duruiheoma

Shugaban ya ce a yanzu yawan al'ummar kasar ya kai miliyan 198, saura milyan biyu ta cika 200

Hukumar Kidiya ta kasa NPC ta ce yawan al'ummar Najeriya ya kusan kai wa miliyan 200.

Shugaban hukumar Mista Eze Duruiheoma ya fitar da wannan sabon adadi ne a ranar Talata a birnin New York na Amurka a wajen taro kan yawan mutane da ci gaba karo na 51.

Shugaban ya ce a yanzu yawan al'ummar kasar ya kai miliyan 198, saura milyan biyu ta cika 200.

Mista Duruiheoma ya ce ana hasashen cewa Najeriya za ta zama kasa ta uku da ta fi yawan al'umma a duniya nan da shekara 30 masu zuwa.

Ya kara da cewa a shekaru 50 da suka shude, yawan jama'a dake zaune a birane a kasar ya karu sosai ba tare da samun karin ababen more rayuwa da zai ishe su ba.

Yayi nuna facin ran sa kan matsaloli tsaro da kuma karancin kayan aiki na kiwon lafiya da mata manya da kanana ke fama da ita wajen haihuwa a kasar.

Yace za'a kula tare da samad da hanyoyi wajen kawo canji da zai taimakawa yan kasa musamman mata wajen kiwon lafiya da cinma burin samad da cigaba a kasar.

Idan ba'a manta ba a kidayar da aka yi cikin shekarar 2006, hukumar ta fitar cewa yawan al'ummar Najeriya ya kai miliyan 140.

Shekaru bayan kidayar, kasar ita ce na bakwai a duniya mai yawan mut wanda hakan ke nufin cewa  daya daga cikin ko wadanne mutum 43 a duniya dan Najeriya ne.

Majalisar dinkin duniya ta yi hasashen cewa Najeriya za ta wuce Pakistan da Brazil da Indonesiya da Amurka a yawan al'umma nan da shkerar 2060, ganin yadda yawan al'ummar kasar ke karuwa.