9jakoloNG

No. 1 Hotspot for Nigerian Music, Video, Sports and Entertainment News


Ali Kwara: Yan sanda tare da taimakon sananen mai farautar barayi sun katse gudun wasu yan fashi da makami, mutum uku sun rasu
PublishedBy: in HausaApril 12, 2018

Mutum uku sun rasu sakamakon musanyar wuta da suka yi

A cewar sakamakon musanyar wuta da suka yi da barayin an raunata wasu guda uku wanda daga baya aka tabbatar da mutuwar su

Rundunar yan sandan jihar Bauchi tare da taimakon sananen mai farautar barayi wato Ali kwara sunyi nasarar dakile wani hari da wasu yan fashi da makami ke shirin kai wa a yankunan jihar.

Yayin da yake ganawa da manema labarai, kakakin rundunar ta jihar Kamal Datti ya bayyana cewa dakarun rundunar da taimakon Ali kwara sun bi sahun yan fashin ne  inda har suka far masu a maboyar su dake dajin Maladunba dake karamar hukumar Misau na jihar.

 

A cewar sakamakon musanyar wuta da suka yi da barayin an raunata wasu guda uku wanda daga baya aka tabbatar da mutuwar su.

An gano wasu bindiga kirar AK-47 guda uku tare da albarusai da bindiga kirar irin ta gargajiya.

Sauran kayayakin da aka gano tare dasu sun hada da harsashin bindigar Double barel da kunshin albarusai na bindigar AK-47 guda uku da mota kira golf mai lamba AH 471 GWA.

An kuma gano adda da kayan unifom na yan sanda guda biyu da kudi naira dubu sha shidda da dari tara (N16,900).


Related Posts:9jakoloNG

Burna Boy – ‘Gbona’

9jakoloNG

Video: Wizkid – ‘Fever’

Leave a Reply Below!

Your email address will not be published.