Army nabs Boko Haram's bomb expert in Gombe

An kama mahadin a garin Kaltungo a shingen bincike da sojoji suka kafa a babban titin Gombe zuwa Yola

Rundunar sojoji ta sanar cewa ta kama wani kwararen mai hada ma kungiyar Boko haram bam-bamai mai suna Adamu Hassan.

Mataimakin kakakin dakarun Operation Lafiya Dole kanal Onyema Nwachukwu, ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ga manema labarai. A cewar sa an kama mai laifin ne a garin Kaltungo dake jihar Gombe yayin da gamayyar sojin da yan sandan farar hula ta DSS ke farautar yan tawaye.

A cewar sa, wanda ake zargi  wanda aka yi wa lakabi da 'Baale' ya shiga hannu ne a shingen bincike da aka kafa a babban titin Gombe zuwa Yola.

A wata labarin da kakakin rundunar na kasa ya fitar, ya bayyana cewa sojin sun kashe wasu mayakan boko haram su uku a wata arangama da suka yi a tsaunin garin Bokko Hilde dake titin Ngoshe zuwa Pulka na jihar Borno.

Sakamakon arangamar da ya faru ranar 9 ga watan Afrilu, sojojin sun kama bindiga kirar AK-47 guda biyu da babur.

Nwachukwu ya kara da cewa a wata aiki da suka kai tare da hadin gwiwar yan banga, sun katse gudun yan boko haram dake sintiri wajen neman abinci da ababen hawa a kauye kudiye dake titin Dikwa zuwa Gulumbagana na jihar Borno.

Yace an samu nasarar dakile harin yan ta'adar bayan sanarwa da aka yi masu na cewa suna nan tafe garin domin kai harin

A bisa bayanin sa yan ta'adar sun bada amsa cewa suna daga cikin tawagar mayakan akidar Abubakar Shekau na kungiyar kuma suma taimakawa da bayanai masu amfani game da yan ta'addar.

Daga karshe yayi kira ga sauran jama'a da su lura da abubuwan dake faruwa a cikin al'ummomin su kuma su sanar da jami'an tsaro cikin hanzari idan idan suka ci karo da abun zargi.