Jaruma Ummah Shehu

Jarumar tayi karin haske Game da furucin da jama'a keyi kan batun cewa yan fim suna bata tarbiya

Jaruma mai tauraro Umma Shehu tayi karin haske game da alakar ta a masana'antar Kannywood da.Tace bata da kawa a farfajiyar fim domin tana gudun duk wani abun da zai bata mata rai.

Hirar ta da wakilin BBC, jarumar wanda hirar ta da Aminu Sheriff Momo a cikin shirin telebijin da yake gabatarwa ya tada kura a kafafen sada zumunta, tace ita bata ji haushin abun da ya faru tsakanin su.

"Ni ban ji haushi ba saboda muna hira ne da Momo akan nishadandartawa ba wai muna hira ne kan addini. duk wanda ya kalli hirar yasan muna wasa ne da dariya a cikin sa".

Jarumar shirin 'sa'insa' tana mai cewa babu kalubalen da ta fuskanta tunda ta shiga masana'antar fim.

Sai dai ta kalubalenci sauran jarumai mata dake masana'antar da su fito a dama dasu wajen shiryawa da daukar nauyin fim.

Ummah Shehu, wacce a harkar shirya fim tana bada himma a ko wani bangare  kama da daga shiryawa, bada umarni, haskawa da neman wuri da dai saura su, tayi kira ga sauran mata da su jajirce wajen shirya fim da kan su maimakon su ringa jira a sasu a fim.

 

Ta bada misalin manyan jarumai mata wadanda suke kan gaba wajen hada fim da kansu irin su Halima Atete, Nafisa Abdullahi, Jamila Nagudu da Aisha Tsamiya, inda ta kara da cewa "don menen mu na kasa dasu baza mu tashi muyi ba?"

Kalaman jama'a kan yan fim suna bata tarbiya

Game da furucin da jama'a keyi kan batun cewa yan fim suna bata tarbiya, jarumar tace bata ganin laifin jama'a domin a nesa suke kallon su. kuma tayi kira na a daina masu kudin goro domin ba duka aka taru aka zama daya ba.

Ta bada misali da jaruma Saratu daso wanda mafi yawanci ana kallon ta da mai mugun hali ganin yanayin fina-finai da take fitowa aciki wanda kuma a zahiri ba haka lamarin yake ba domin "Ita Daso mutum ce wanda idan ka zauna da ita zaka so ka kara zama da ita".

"Bana ganin laifin su, domin a nesa suke kallon mu. Abun da suke gani a Telebijin shi suke daukawa. Idan yau aka ce Umma Shehu yar iska ce, toh Umma Shehu ya kamata a zaga ba kaf yan fim ba".

Masu satar fasaha

Daga karshe jarumar ta nuna bacin ran ta game da masu satar fasaha.

"Tsakanin mu da yan faresi Allah ya isa. Su ci haram, su sha haram, su cirar da iyalen su a haram".

A cewar ta, masu satar fasaha suna sata ne ba tare da duba irin kudin da aka dauka wajen shirya fim kana su siyar a cikin kaskantacen kudi.