9jakoloNG

No. 1 Hotspot for Nigerian Music, Video, Sports and Entertainment News


’Apr’
’11’
Muhammadu Buhari: Jerin sunayen sabbin shugabannin hukumomin gwamnati da shugaban kasa ya nada
PublishedBy: in HausaApril 11, 2018

7 reasons why president declared for 2nd term

Hukumomin sun hada hukumar zabe na kasa da ma'aikatar lafiya da ma'aikatan labarai da al'ada tare da ma'aikatar ilimi da kuma ma'aikatar wuta, ayyuka da gidaje

Shugaba Muhammad Buhari ya yi sabbin nade-nade kafin ya garzaya kasar Ingila na shugabannin wasu hukumomin gwamnati.

Hukumomin sun hada hukumar zabe na kasa da ma'aikatar lafiya da ma'aikatan labarai da al'ada tare da ma'aikatar ilimi da kuma ma'aikatar wuta, ayyuka da gidaje.

Sanarwar nadin ya fito ne a wata takardar sanarwa da Mista Lawrence Ojabo, daraktan labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya fitar ga manema labarai

Ga jerin sunayen su da kuma mukamin da aka nada masu kamar haka:

Dakta Abdulkarim Yusuf – matsayin daraktan asibitin masu tabin hankali da ke Kaduna

Dakta Abubakar Musa – daraktan cibiyar lafiya ta tarayya da ke Nguru

Dakta Abdullahi Ibrahim – daraktan cibiyar lafiya ta tarayya da ke Azare.

Dakta Illiasu Ahmed  – daraktan cibiyar lafiya ta tarayya da ke Owo sauran su ne

Dakta Nasir Umar –  Shugaban cibiyar NOFC da ke Bauchi

Dakta Aliyu El-ladan – Shugaban cibiyar NOFC, da ke Katsina

Dakta Stella Oyedepo –  Babbar manajar Gidan Wasanni da ke Legas

Dakta Baba Danjuma –  Shugaban Kwalejin Kimiyya da ke Idah.

Dakta Usman Kallamu –  Shugaban Kwalejin Kimiyya da ke Damaturu,

Dakta Jimah Sanusi – Shugaban Kwalejin Kimiyya da ke Auchi

Dakta Dayo Oladebeye – Shugaban kwalejin Kimiyya da ke ado-Ekiti

Sanusi Gumau – Shugaban kwalejin Kimiyya da ke Bauchi

Farfesa Tomunomi Abbey –  Shugaban kwalejin Kimiyya da ke Bonny.

Faruk Haruna – Shugaban kwalejin horas da malamai ta Kontagora

Omokungbe Omoseni – Shugaban kwalejin Kimiyya da ke Yaba

Usman Mohammed – a matsayin babban darakta mai kula da ayukan kamfanin ma'aikatar aiki, wuta da gidaje na tarayya

sauran sun hada da Emmanuel Alex Hart, Mohammed Magaji Ibrahim, Dr. Cyril Omorogbe, Dr. Uthman Abdulrahman Ajidaba, Segun Agbaje, Baba Abba Yusuf da Yahaya Bello wadanda aka nada a matsayin kwamishinonin zabe.

Shugaban ya umurci su da su jajirce wajen aiwatar da aikin su a ma'aikatan su domin kawo sauyi cikin adalci da nagarta.

Support 9JAKOLO NG' journalism of integrity and credibility

 

Good journalism costs a lot of money. Yet only good journalism can ensure the possibility of a good society, an accountable democracy, and a transparent government.

For continued free access to the best investigative journalism in the country we ask you to consider making a modest support to this noble endeavour.

By contributing to 9JAKOLO NG, you are helping to sustain a journalism of relevance and ensuring it remains free and available to all.

Donate

Related Posts


9jakoloNG

Larry Gaaga feat. Wizkid – Low

9jakoloNG

Video: Kehlani feat. 6LACK – RPG

Comment Below!

Your email address will not be published.